Najeriya ma tabi sahun sauran kasashen wajen dake gudanar da wannan biki ta yin taruka da bayyana muhimmancin ruwan sha mai tsafta. Hakan yasa wakilin Muryar Amurka dake jihar Lagos, Salihu Jibril, ya ji ta bakin wasu mazauna birnin da kuma gwamnatin jihar akan kokarin da suke na samar da ruwan sha.
Babban sakatare a hukumar samar da ruwan sha a jihar Lagos, Kabiru Ahmed Abdullahi, yace suna iya kokarinsu na ganin sun samar da ruwan sha, duk da yake abune mai kunshe da kalubale, amma ana tunkarar hanyar da za a samar.
A shekarar 1992 ne a wajen wani taron Majalisar Dinkin Duniya akan ingantar muhalli da kuma ci gaban kasa da aka gudanar a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, aka ware wannan rana domin bukin ranar ruwa ta duniya.
Domin karin bayani saurari rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5