Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kammala taron zaman lafiy da hukumar addinin musulunci ta duniya ta shirya a Abuja


Hoton taron kungiyar addinin musulunci ta duniya da aka yi a Abuja
Hoton taron kungiyar addinin musulunci ta duniya da aka yi a Abuja

A taron yaki da ta'adanci da zaman lafiya da hukumar addinin musulunci ta duniya ta shirya a Abuja wadda shugaba Buhari ya bude shugaban kungiyar Shaikh Abdulmuhsin Al-Turki yace wajibi ne musulmi su dage wajen fahimtar hakikanin koyaswar addinin musulunci

Yayinda ake kammala taron jiya a Abuja shugaban hukumar na duniya Abdulmuhsin Al-Turki yace matsalolin da ake gani sun bijiro ne saboda raunin da musulmai suka samu da ya kawo rarrabuwa tsakaninsu har wasu suka samu gurbatacciya akida da ta sanyasu zarmewa.

Shugaban majalisar musulunci na duniya Shaikh Al-Turki shi ya yi magana akan zaman lafiya a taron. Ya yabawa musulmin da suka taru domin fahimtar addini akan gurbatacciyar akidar Boko Haram da suka shiga harbe-harbe sakamakon barin addinin musulunci da mutunta dan Adam bisa dokokin Allah.

Muhammad Umar Nijallo da ya zo daga kasar Ghana yace ilimi kamar kasa yake baya karewa saboda haka malami dake koyas da addinin musulunci ya kasance yana samun karuwa. Abu na biye dashi ya kamata malami ya san yadda zai jawo al'umma su fahimci addinin musulunci tsantsa dalili ke nan aka tara manyan malamai daga kasashen Afirka domin a koyas dasu.

An kira 'yan darika taro irinsu IZALA ko zasu daina yin diran mikiya. Abdullahi Digi babban jami'in kungiyar IZALA yace su suna fadan abun da littafi ya fada ne tsakaninsu da Allah. Wadanda suka zarmaye 'yanuwa ne musulmai kuma ana son a kirasu domin a samu fahimta. Dalili ke nan suka gayyaci Alhaji Yahaya Jingir da bangarensa amma basu kasance wurn ba.

Kafin a rufe taron shugaban IZALA Alhaji Bala Lau ya nemi a dinga yiwa gwamnatin tarayya addu'a kan yaki da cin hanci da rashawa tare da gamawa da Boko Haram.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG