An dai gudanar da zaben ne a wani yanayi da wasu ke kwatantawa a matsayin zabe mafi inganci a tarihin kasar.
Akalla masu kada kuri’a miliyan biyar suka garzaya rumfunan zabe domin fidda da mutum guda cikin ‘yan takarar shugaban kasa 14, a wannan zabe da masu fashin baki suka ce babu wata alama da ke nuna ga wanda zai lashe zaben.
Idan dai har ba a samu wanda ya lashe akalla kashi 50 na kuri’un da aka kada ba, to za a je zagaye na biyu.
Tsohon shugaban kasar Blaise Campoare ya mulki kasar ta Burkina Faso na tsawon shekaru 27, kafin ya yi yunkurin yin garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar, domin kawar
da tsarin kayyade wa’adi ga shugaban kasa, wanda hakan zai bashi sake mulkar kasar.
Wannan yunkuri ya haifar da bore a duk fadin kasar, lamarin da ya tilasta mai ajiye mulkin daga bisani.
An dai kafa wata gwamnatin wucin gadi da ta maye ta Shugaba Campoare, inda aka ayyana cewa za a yi zabe a watan Oktoban da ya gabata, sai dai wani dan takaitaccen juyin mulki da bai yi nasara ba, ya sa aka dage zaben zuwa wannan wata.