Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsugune Bai Kare Ba a Burkina Faso


 Michel Kafando shugaban Burkina Faso na rikon kwarya
Michel Kafando shugaban Burkina Faso na rikon kwarya

Gwamnatin Burkina Faso tace tana nan tana lallabar Janar din nan da ya jagoranci juyin mulkin da bai yi karko ba, don ya mika wuya.

Wannan magana ta fito ne kwana daya rak da ya nemi mafaka a wani ofishin jakadanci a babban birnin kasar.

Sanarwar tace, ana kan hanyar kulla yarjejeniya domin Janar Gilbert Diendere ya yarda ya mika wuya ga hukumomin mulkin kasar.

Sanarwar ba ta nuna takamaiman ofishin jakadancin da yake ba, sai dai rahotannin Reuters sun ce yana boye a wata harabar ofishin jakadancin Paparoma a birnin Ouagadougou.

Gwamnati tace sai da sojojinsu suka caje sansanin masu tsaron shugaban kasar wato RSP da Diendere ya ke jagoranta kafin a cire shi a makon jiya.

Sannan suka kwace sansanin nasu bayan wata gajeriyar fafatawa. Sojojin kasar na neman RSP da su ajiye makamansu a matsayin bangaren yarjejeniyar sasantawa.

Janar Gilbert ya bayyana a wani gidan radiyon kasar shekaran jiya Talata yana kira ga sojojin da ke masa biyayya da su ajiye makamansu.

XS
SM
MD
LG