Sojoji su fatattaki masu zanga zangar a Masar

Masu zanga zangar a Masar suke kokarin kare kansu, a arangama da jami'an tsaro.

Yau Lahadi kwana uku a jere ke nan, masu zanga zangar da jami’an tsaro suke arangama a Masar. An kashe mutane goma kuma daruruwa sunji rauni tun lokacinda aka fara wannan tarzoma a ranar juma’a.

Yau Lahadi kwana uku a jere ke nan, masu zanga zangar da jami’an tsaro suke arangama a Masar. An kashe mutane goma kuma daruruwa sunji rauni tun lokacinda aka fara wannan tarzoma a ranar juma’a.

Sojoji sun fatattaki masu zanga zangar wadanda ke jifa da duwatsu a lokacinda suka yi kokarin taruwa a dandalin Tahrir a birnin Alkahira. Wasu masu zanga zangar sun sa shingaye domin kariya.

Su dai masu zanga zangar suna bukatar nan da nan sojojin dake jan ragamar mulkin kasar suyi murabus.

Wannan tarzoma ta biyo bayan zagaye na biyu na zaben wakilan Majalisar wakilan kasar, zaben farko tun lokacinda aka hambarar da gwamnati Hosni Mubarak a watan fabrairu.

Kamfanin dilancin labarum kasar da ake cewa MENA a takaice, ya bada labarin cewa, da alama jam’iyun Muslim Brotherhood da Al Nour Salafi sune suka lashe yawancin kujeru a zaben da aka yi a ranar litinin da talata. Dama kuwa wadannan jam’iyu guda biyu sune ,suka kanainaiye zagaye na farko na zaben da aka yi.

Majalisar mulkin soja ta kasar tace zata sauka daga kan ragamar mulki da zarar an zabi sabon shugaba a karshen watan Yuni idan Allah ya kaimu.

Aika Sharhinka