Dubban ‘yan Masar ne suka yi gangami a Alkahira da wasu birane masu yawa, suna neman majalisar soja dake mulkin wucin gadin kasar, ta nemi gafara kan irin cin zarafin da suka yi wa mata da suka fito suna zanga-zanga.
Gangamin na Jumma’a da aka lakabawa sunan “Jumma’ar maido da martaba”. Hakan ya biyo bayan mako da aka kashe akalla mutane 17 masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati, a arangama da jami’an tsaro.
‘Yan Masar da dama sun fusata bayan sun kalli vidiyo da ya nuna sojoji suna dukan wata mace dake zanga-zanga, suna jan ta a kasa.
Wata mace Samah Ibrahim, wacce ta fito zanga-zangar yau, tace tarzomar bata tsorata ta ba.
Majalisar mulkin sojan kasar ta bayyana “takaicin” aukuwar lamarin, kuma tace zata dauki matakan shari’a kan wadan da suke da hanu a wan nan lamari.
Ahalin yanzu kuma wasu magoya bayan majalisar mulkin sojin kasar sun yi nasu gangami a wani bangaren birnin na Alkahira.