Yau Ce Ranar Zaman Lafiya

Alama ko kuma tambarin tsuntsu da ke nuna muhimmancin zaman lafiya

21 ga watan Satumbar kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin kara fadakar da jama'a kan muhimmancin zaman lafiya a duk fadin duniya.

Taken wannan shekara shi ne samar da hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kuma mutunta kowa da kowa.

Jahar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, na daga cikin juhohin da ke fama da rikici musamman abin da ya shafi raddnin da kabilanci ko kuma tsakanin manoma da makiyaya.

“Na daya akwai barna ta gangaci, wanda za a shiga gona a bata ta baki daya, sannan akwai kashe- kashe wanda za a aje kauye a fada kan mata da kanana yara, sannan akwai satan shanu, duk abubuwan nan su suke kawo rikici a wannan karamar hukuma” In ji Da Edward Gyang Bot, wani shugaban al’uma a karamar hukumar Barkin Ladi da ke Jahar Filaton.

Shi kuwa Ustaz Alhaji Ibrahim cewa ya yi rikicin na samo asali ne saboda yadda mutane suke daukan doka a hanunsu ba tare da an hukunta su ba.

“Duk rikicin nan tsakanin makiyaya ne da manoma daga baya sai kaga ya rikide ya koma na addini, duk mutumin da aka same shi ya shiga gonar wani ko kuma wani ya harbi shanun wani ya ko ya kora su a matsayin ya sace su, sai a hukunta shi, domin babu wanda ya gagari gwamnati.” In ji Ustaz Ibrahim.

Shugabannin addinai suma sun yi kira wajen ganin an hada kai domin tabbatar da dorewar zaman lafiya ba tare da an samu baraka ba.

Saurari tsokacin shugaban JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, da na mataimakin sakataren darikar ECWA Elyasa Baba a karshen wannan rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Yau Ce Ranar Zaman Lafiya 3’46”