Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Burkina Faso Sojoji Na Garkuwa da Shugaban Kasar da Firayim Minista


 Masu zanga zanga Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, 16 Septembre, 2015 dangane da garkuwar da wasu sojoji suka yi da shugabannin kasar
Masu zanga zanga Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, 16 Septembre, 2015 dangane da garkuwar da wasu sojoji suka yi da shugabannin kasar

A jiya Laraba wasu sojoji da ke tsaron shugaban kasa a Burkina Faso sun tsare Firaminista da shugaban kasar masu rikon kwarya da aka ce sun yi garkuwa da su.

Majiyoyin sojojin kasar sun fadawa Sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa, sojojin sun kutsa kai ne a lokacin da ake tsakiyar taron Majalisar Ministocin kasar.

Sun kuma kama Shugaban kasar Michel Kafando da Firaminista Yacouba Isaac Zida da wasu ministoci.

Ba’a baiwa wadanda aka kama din damar fita ba daga zauren taron, sannan kuma an ga sojoji suna ta kafa shingaye a harabar fadar shugaban kasar.

Sa’o’i kadan kuma an ji karar harbe-harben bindiga a lokacin da ake kokarin tarwatsa masu zanga-zanga zuwa fadar shugaban kasar.

Ba dai wani bayanin da ya nuna wasu sun jikata. Shugaban hukumar mika mulki Cherif Sy, yayi Allah wadai da wannan mamaya.

Sannan yace ana rike da mutane 4 a ciki har da Shugaban Kasa da Firaministan. Yace, ‘’Ina kira ga duk ‘yan kishin kasa da su tashi mu ceci kasarmu ta haihuwa.’’

Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar kasashen Afirka da kuma kungiyar habaka tattalin arzikin Afirka ta Yamma sun bukaci a saki wadanda aka yi garkuwar da su.

Sun kuma kira abin a matsayin kamen da ba abin amincewa ba ne. sojojin dai har yanzu ba a san su wanene ba. Basu kuma bayyana wata bukata ba.

Wannan abu ya faru ne a kasa da wata dayan da ya rage a yi zaben Shugaban Kasar da na ‘yan Majalisa.

An dai sa yin zaben na shugaban kasa tsakanin shugaban gwamnatin rikon kwarya da sojojin da aka fi sani da lakani RSP.

XS
SM
MD
LG