Dr Muhammad El-Nur Dengel kwararre akan harkokin tsaro na Jami'ar Maiduguri yace tunda 'yan kungiyar sun soma bada kansu yakamata a yi masu binciken kwakwaf saboda a san abun da suka sani.
Masanin yana ganin akwai wadanda ba zasu bada kansu ba kuma wadanda ma suka fito din wasu sun yi hakan ne domin basu da zabi. Wajibi ne a tantancesu a samu duk bayanan da zasu yi taimako.
Yakamata a san wadanda suke mara wa kungiyar baya. Dole ne a zakulo iyayen gidansu. Sanin wadannan abubuwan zai taimakawa kasar.
Kakakin hedkwatar sojin Najeriya Kanal Sani Usman Kukasheka yace su sojoji basu da wani matsayi akan 'yan Boko Haram dake mika kansu sai abun da gwamnatin tarayya ta yi da shawarar da ta yanke kansu.
Kanal Kukasheka yace amma suna da kwararru su ne zasu binciki mutanen bayan haka kuma akwai wasu kaidoji na aiki da dole za'a bi.
Yace har yanzu suna karbarsu kuma zasu cigaba da yin hakan.
To saidai Dr Muhammad Dengel ya yi tsokaci dangane da yadda 'yan kungiyar Boko Haram din ke mika kansu ga jami'an soji. Yace duk wadanda suka yi laifi bai kamata a barsu ba saboda sun bada kansu ne domin basu da wata mafita.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.