Therese May ta bukaci ayi zaben tun da wuri shekaru uku kafin wa’adi wakilan Majalisar dokokin kasar ya cika. Tunda farko Fara Ministar ta sa ran jam’iyar ta ta Conservative ta samu rinjaye sosai a Majalisar, to amma wannan hasashe sai ya dakushe bayan yakin neman zaben ta ya fuskanci matsala a yan makonin da suka shige.
Kididdigar jin ra’ayin jama’a da dama da aka yi sun nuna jam’iyar Labour ta masu hamaiya tana samun karin farin jinni akan jamiyar ta Conservative.
Dukkan kujeru dari shidda da hamsin na Majalisar wakilan kasar ne ake takara su a zaben na yau Alhamis. Jam’iya tana bukatar lashe kujeru dari uku da ashirin da shidda domin ta samu sukunin kafa gwamnatin masu rinjaye.
Munanan hare hare ta’adanci a aka kai a kasar sun dakushe matakin karshe na yakin neman zabe da ake yi a kasar.