Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Ya Kai Hari a Faransa Dan Asalin Aljeriya Ne


A jiya Talata, Ministan harkokin cikin gida na Faransa Gerard Collomb, ya ce mutumin da ya kaiwa ‘dan Sanda hari da guduma a harabar cocin Notre Dame a Paris, yayi ihun cewa “hakan ramuwa ce ga Syria.”

Minista Collumb, ya fadawa manema labarai cewa katin sheda da aka samu a jikin maharin ya nuna cewa shi dalibi ne dan asalin kasar Aljeriya.

Ofishin lauyan gwamnatin Faransa, ya ce bangaren yaki da ta'addanci na ofishin ya fara bincike kan harin, wanda ya auku a daidai lokacin da 'Yan Sanda suke sintiri a harabar cocin, da masu yawon bude ido ke zuwa.

Rundunar 'Yansanda ta birnin Paris tace wani ‘dan Sanda ya harbi maharin ya jikkata shi bayan da ya kai hari da guduma a kan wani ‘dan Sandan.

Minista Collumb, ya ce maharin kuma yana dauke da wuka irin ta aikin gida, wanda hakan ke nuna cewa wani nau’in kai hare-hare ne na ta’addanci, wadanda ke amfani da duk makamin da suka samu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG