Sanarwar da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na twitte, na zuwa ne kwana guda kafin Comey, wanda Trump ya kora a aiki a watan da ya gabata, ke shirin bayyana a gaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar Dattawa domin ba da bahasi.
Ana sa ran za a yi mai tambayoyi kan zargin cewa Trump ya yi yunkurin hana shi gudanar da bincike kan zargin cewa a gangamin yakin neman zaben shi shugaba Trump, ya hada kai da kasar Rasha.
Shi dai zabin na Trump, wato Wray, ya taba shugabantar sashen dake kula da hukunta manyan laifuka daga shekarar 2003 zuwa 2005 a lokacin zamanin tsohon shugaban Amurka, George W. Bush.
Yanzu haka yana aiki ne a wani kamfanin hadakar lauyoyi na King and Spalding mai zaman kansa, inda yake rike da matsayin mai kare wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka.
Facebook Forum