Kamfanin Dillancin Labaran kasar Iran, ya ruwaito a yau Laraba cewa, hare-haren sun kaikaici majalisar dokokin kasar ne da kuma wani wajen ibada na marigayi shugaban addini, Ayatollah Ruhollah Khomeini.
Rahotannin sun ce wasu ‘yan bindiga uku da wani dan kunar bakin wake ne suka kai hare-haren, ciki har da na wajen ibadar, dake kudancin birnin Tehran, inda mutane da dama suka ji rauni.
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun kama akalla mutum guda daga cikin maharan.
A harin na Majalisar dokokin kasar, rahotannin sun ce an samu bayanai masu karo da juna, inda wasu suka ce akalla ‘yan bindiga hudu ne suka ka yi ta harbe-harbe, inda mutum guda ya mutu sannan wasu da dama suka ji rauni ciki har da wani mai gadi.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kashe akalla mahara shida daga cikin ‘yan bindigar wadanda mafi yawansu suka yi shigar mata domin badda kama.
Wannan shi ne karon farko da bangaren Musulmi na Sunni ya fito fili ya dauki alhakin kai hari a kasar ta Iran wacce mafiya rinjayenta mabiya akidar Shi’a ne.
Facebook Forum