Manyan kusoshin gwamnati tare da shugaba Muhammad Buhari suka yi ganawa ta musamman da 'yan matan a gaban daruruwan 'yan jarida.
Shugaba Buhari ya gana da kowace cikin 'yan matan tare da iyayensu da malamansu da shugaban al'ummarsu.
A jawabinsa da yayi masu shugaban yace ukubar da suka sha a hannu 'yan Boko Haram ita ce makura ta cutar da bil Adama na ganawa mutum azaba. Saboda haka shugaban yace gwamnatin Najeriya zata yi dukan kokarin da zata iya yi ta tabbatar ta shafe hawaye kukansu, ta basu lagwadar duk duniya wadda zata sabawa irin ukubar da suka sha a hannun 'yan Boko Haram.
Abun da gwamnati zata yi ya hada da daukan nauyin iliminsu da zamansu da rayuwarsu baki daya.
Saboda farin ciki 'yan matan sai da suka yi wake wake nan take bayan alkawuran da shugaban kasa yayi masu.
Idan aka kwatanta fuskokinsu yau da ranar da aka shigo dasu, ko shakka babu 'yan matan sun murmure kuma suna kan murmurewa. Lokacin da aka shigo dasu Abuja sun kanjame. Amma yanzu annuri ya fara dawowa fuskokinsu.
Ga firar da abokin aiki Mahmud Lalo yayi da Umar Faruk Musa da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5