Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Murnar Iyayen 'Yan Matan Chibok Da Suka Sami 'Yanci


A jiya ne, a Najeriya, iyayen wasu daga cikin ‘yan matan Chibok da suka sami ‘yancin kansu, suka yi ta tsallen murna bayan da aka maido musu ‘ya’yan nasu da yan ta’adda suka sace, kuma suka yi garkuwa da su sama da shekaru biyu.

A shekarar 2014 ne akayi awon gaba da kusan yaran mata 300 na makarantar Chibok dake jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, wurin da ya sha fama da rikicin Boko Haram da suka yi kokarin kafa daular musulunci, inda kuma aka kashe dubban mutane, wasu sama da miliyon biyu kuma suka rasa matsugunansu.

A makon da ya gabata ne, yan tawayen suka sako 21 daga cikin ‘yan matan a dalilin shiga-tsakanin kungiyar bada agaji ta Red Cross da kuma gwamnatin Switzerland.

An sako yan mata ne a ranar Alhamis kuma aka kaisu birnin Abuja ta sama, sai dai ya dauki wasu yan kwanaki kafin iyayensu su iya isowa Abujar daga yankunansu na karkara.

Koda yake ‘yan matan da dama da aka sace sun sami sa’ar arcewa bayan da aka sace su, har yanzu akwai sauran ‘yan mata 197 a hannun yan tawayen.

Gwamnatin ta Najeriya dai tace tana ci gaba da tattaunawa don ceto sauran ‘yan matan.

XS
SM
MD
LG