Jami'an Najeriya sun ce an sako 21 daga cikin daolibai 'yan mata na Chibok wadanda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a shekarar 2014.
Wani kakakin shugaba Muhammadu Buhari ya fada ta shafinsa na Twitter a yau alhamis cewa wadannan 'yan mata su 21 su na hannun Hukumar Tsaron Cikin Gida ta DSS.
Mallam Garba Shehu yace an sako wadannan 'yan matan ne a sakamakon tattaunawa tasakanin gwamnatin shugaba Buhari da 'yan kungiyar Boko Haram. Kungiyar agaji ta Red Cross da kuma gwamnatin kasar Switzerland sune suka shiga tsakani a wannan tattaunawa.
Yace za a ci gaba da tattaunawa kan sauran 'yan matan da ake tsare da su, yana mai cewa za a mika wadannan dalibai ga mataimakin shugaba Yemi Osinbajo, a kuma bayyana sunayensu nan ba da jimawa ba.
Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ambaci wani jami'in sojan Najeriya yana fadin cewa an musanya wadannan 'yan mata su 21 ne da wasu shugabannin Boko Haram su 4 da ake tsare da su.