Yarima Bin Salman Na Shirin Kai Ziyara A Pakistan

Shugabannin Saudiya da na Pakistan

Yarima mai jirar gado a Saudi Arabia Mohammed bin Salman zai fara wata ziyarar wuni biyu ta farko zuwa Pakistan a yau Lahadi, inda ake sa ran zai sanar da wani aikin zuba jari na biliyoyin daloli.

Wannan babbar ziyara da ba a saba gani ba, tana zuwa ne a lokacin da Pakistan keda hadari na tsananin tankiya tsakanin ta da babbar kishiyar ta kasar India a kan wani mummunar harin kunar bakin wake da aka kai a makon da ya gabata a yankin Kashmir da ake takaddama a kai.

New Delhi ta zargi Islamabad da taka rawa a wannan harin da ya kashe sama da jami’an tsaron India 40, wani zargi da jami’an Pakistan suka musunta kuma suka ce bashi da tushi.

Yarima bin Salaman mai lakabi MBS atakaice, zai yi ziyarar ce da wata babbar tawaga, ciki har da iyalan gidana sarauta da wasu manyan minstoci da kuma manyan ‘yan kasuwa 35. An kuma shirya Yarimar zai gana da Firai Ministan kasar Imran Khan da babban sojojin Pakistan Janar Qatar Javed Bajwa.