Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Rohingya Na Bukatar Daukin Gaggawa


ဘဂၤလားေဒ့ရွ္ေရာက္ ႐ိုဟင္ဂ်ာဒုကၡသည္မိသားစု (ဓာတ္ပံု-ကုလသမဂၢ)
ဘဂၤလားေဒ့ရွ္ေရာက္ ႐ိုဟင္ဂ်ာဒုကၡသည္မိသားစု (ဓာတ္ပံု-ကုလသမဂၢ)

Hukumar agaji ta majalissar dinkin duniya ta na neman dala miliyan $920 don samar da kayan agaji na ceton rayukan ‘yan gudun Hijirar Rohinja sama da dubu dari tara (900,000), wadanda su ka tsere zuwa Bangledesh don kaucema tashin hankali da tsanani a Myanmar.

Akasarin ‘yan Rohinja na zama a takure da kuma mawuyacin hali a sansanin ‘yan gudun hijira da ake kira da Kutupalong, wanda shine sansanin ‘yan gudin hijira a duniya mafi girma.

Hukumomin Bangladash sun sha yabo sabodo ansar ‘yan gudun Hijira masu yawa. To amma Ministan Harkokin Wajan Bangledesh, Shahriar Alam, ya amasa cewa akwai matsala sosai.

Alam ya ce, mafuta itace a maida su kasashen su. Ya ce Bangladesh ta sha tattaunawa da cibiyoyin majalissar dinkin duniya kan wannan zabin. Bara, majalissar dinkin duniya da gwamnatin Myanmar sun saka hannun kan maida ‘yan Rohinja kasar su.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG