Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, ta gana na dan wani lokaci da wani rukunin Amurkawa yan asalin kasashen larabawa a Flint na Michigan a ranar Juma’a, da nufin samun goyon bayan al’ummomin da suka kullaci irin rawar da gwamnatin Amurkan ke takawa a yakin da ake yi a Gaza, da ya fadada zuwa Lebanon.
Kwamitin yakin neman zaben ta ya fada cikin wata sanarwa cewa, mataimakiyar shugabar kasar ta ji ta bakin al’ummar kai tsaye kan yadda suke kallon zaben da kuma tashin hankalin da akeyi a Gaza da Lebanon.
Sanarwar ta kara da cewa, Harris ta bayyana damuwar ta kan irin halin kuncin da al’ummar Gaza ke ciki, ta kuma tattauna kan irin kokarin ta na ganin an kawo karshen yakin, tare da kaucema ballewar yaki a yankin.
Dangane da Lebanon kuwa, Harris ta bayyana damuwa kan lamarin farar hular da ake kashewa tare da jikkatawa, da ma wadanda aka raba da muhallan su, inda ta jaddada kudurin gwamnati nayin amfani da diplomasiyya wajen magance matsalar, domin cimma zaman lafiya da bayar da kariya ga farar hula.
Jihar Michigar fagen daga ne a zabe, dake da al’ummar Amurkawa yan asalin kasashen Larabawa kusan dubu 400, mafi girma a kasar idan aka kasa bisa 100, cewar cibiyar Amurkawa yan asalin kasashen Lrabawa.
Da bangaren yakin neman zaben Harris din, da ofishin mataimakin shugaban kasar ba wanda ya samar da jerin sunayen wadanda zasu shiga a dama da su. To sai dai duk da haka, shugaban rundunar sa kai kan Lebanon, Edwrd Gabriel, yace, ya shiga cikin taron da akayi. Yace sun tattauna batun tsagaita wuta, da bukatar dake akwai ga Amurka da kawayen ta na ganin sun magance batun matsalar taimakon jin kai.
Haka zalika wakilan kungiyar yada manufofin musulunci ta Amerika na Emgage, sun tabbatar da amincewa da Harris tun a watan Satumba, yayin da suka bayyana fargabar su kan irin mulkin kama karyar da Trump ke aniyar yi kan musulmin Amerika, Amurkawa da ma duniya baki daya.