Kanfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, Babban sakateren ya bayyana damuwa matuka a game da ta’azarar rikicin na Sudan, wanda yake ci gaba daidaita rayuwar fararen hula ‘yan Sudan sannan yake tattare da hadarin yiwuwar bazuwa a yankin” Kamar yadda wata sanarwar ganawar da Guterres ya yi da Abdel-Fatah Al-Burhan ta kunsa.
A wani bangaren kuma, Amurka za ta bai wa al’ummar Sudan karin kudin tallafin agajin jin-kai na dala $424, abin da jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas Greenfield ta sanar a ranar Laraba kenan.
A tsakiyar watan Afirilun bara ne yakin ya barke a sanadiyyar rikicin neman iko tsakanin sojojin sojin kasar ta Sudan SAF da kuma mayakan Rapid Response Support Force gabann shirin mika mulki ga mulkinfararhula a kasar.
Sama da ‘yan Sudan miliyan 25 ne suke fuskantar mummunar matsalar yunwa.
Da dama daga cikin su suna fama da rashin abinci (yunwa) sannan wasu miliyan 11 kuma sun gudu daga gidajensu a wani yanayi da ya zama babbar matsalar jin-kai mafi muni a duniya a cewar Ambassada Thomas-Greenfield.
“Wajibi ne bangarorin biyu da ba sa ga maciji su amince su jinkirta fadan bisa dalilin bukatu na jin-kai a al-Fashir, Khartoum da sauran yankunan da suke cikin mumunan yanayin bukata.
Wakilin Reuters Michelle Nicholas ya ruwaito cewa, Sanarwar ta ce jumullar kudaden da Amurka ta kashe don ba da tallafin jin-kai tun daga farkon rikicin ya kai dala biliyan$2, a bayanan ofishin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya.
Dandalin Mu Tattauna