Yanzu a Nigeria duk wanda ya saba dokoki ko matakan hana bazuwar cutar korona bairos zai je gidan yari na watanni shida. Wannan tanajin hukuncin na kunshe a sabuwar dokar Shugaban ‘kasa mai lamba ta 4 wadda shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba ma hannu a Abuja. Ministan shari’a kuma Attoni-Janar, Abubakar Malami ya yi wa wakilinmu, Umar Farouk Musa ‘karin bayani.
Amma a cewar Ministan, Shugaba Buhari ya bai wa Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yado ta Najeriya damar yin kwaskwarima ma dokar ta Shugaban Kasa idan bukatar hakan ta taso. Dalilin hakan kuwa, inji Minista Malami, shi ne ana iya samun sauyi a tsananin cutar. Don haka, ya ce, kamata ya yi tsananin dokar ta yi daidai kuma da tsananin cutar a kowani lokaci.
Ya ba da misali cewa, idan aka samu wani yanayin da rashin saka takunkumin rufe fuska ba zai zama da hadari ba, wannan hukuma na iya saukaka ma mutane da sanya takunkumin bisa ganin dama. Ya ce haka kuma idan ta yi tsanani sai ita ma dokar ta yi tsanani. Hikimar hakan, inji Ministan, shi ne aga cewa ‘yan kasa ba su cutu ba a kowane hali.
Da aka tambaye shi yadda dokar za ta shafi mutumin da ke cikin motarsa ko wani kebabben wuri shi kadai, sai ya ce adalcin doka ya bai wa mutumin da ke kebe shi kadai, ta yadda ba zai iya kamuwa da cutar ko ya yada ta ga wasu ba, damar walwala.
Ya ce za a aiwatar da dokar da kuma zartar da hukuncinta ne babu sani ba sabo.
Saurari cikakkiyar hirar Umar Faruk da Minista Malami:
Your browser doesn’t support HTML5