IMF ta ce tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 5.5 a wannan shekara, sama da hasashen da hukumar ta yi na kashi 5.2 a watan Oktoban da ya gabata, yayin da riga-kafin cutar ke taimakawa wajen dakilke yaduwar coronavirus.
Hakan a cewar IMF, ya taimakawa gwamnatoci wajen sasssauta matakan kulle da suka saka a bara wadanda suka haifar da tarnaki ga tattalin arziki wanda rabon da a ga irinsa tun bayan yakin duniya na biyu.
Wannan hasashe na IMF na ganin karin kashi 5.5 a tattalin arzikin duniya, zai kasance mafi sauri tun bayan wanda aka gani na farfadowar komadar tattalin arziki na 2010.
Yayin da ake fatan riga-kafin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya, hukumar lamunin ta IMF ta yi gargadin cewa tattalin arzikin duniyar na bukatar tallafi daga gwamnatoci domin rage illar da annobar ta yi.