Ta yiwu yankin Catalonia dake kasar Spain da ya jefa kuri’ar raba gardamar samun ‘yancin kai ranar Lahadi a lokacin da ‘yan sandan kasar suka yi kokarin murkushe masu jefa kuri'a, ya ayyana ‘yancin cin gashin kai a karshen makon nan ko kuma mako mai zuwa.
WASHINGTON D.C. —
Carles Puigdemont, shugaban yankin, ya fadawa kafar yada labaran Ingila, ta BBC cewa, gwamnatin yankin zata dauki wani mataki da zarar an kammala kirgar kuri’u.
Puigdemont na shirin gabatar da jawabi yau Laraba da yamma.
Hukumomin Catalonia sun ce kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kada kuri’a ranar Lahadi na so su balle daga kasar Spain su ayyana kafa Janhuriyarsu.
A wasu lokutan masu kada kuri’a sun yi bajintar kaucewa yinkurin ‘yan sandan kasar na rufe rumfunan zabe da hana ‘yan kasar Catalonia kada kuri’ar raba gardama, abinda kotun kolin kasar Spain a baya ta ce ya saba ka’ida.