Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Spain Yayi Allah Wadai da Zaben da Yankin Catalonia Ya Shirya Ranar Lahadi


'Yan yankin Catalonia da suka kada kuri'ar ballewa daga kasar Spain
'Yan yankin Catalonia da suka kada kuri'ar ballewa daga kasar Spain

Bayan gudanar da zaben amincewa da ballewa da 'yan yankin Catalonia suka yi ranar Lahadi sarkin Spain ya fito karara ya yi Allah awadai da zaben

Sarkin Spain na Shida, Felipe ya yi Allah wadai da hukumomin Catalan, yana mi cewa sun take doka, bayan da suka gudanar da zaben raba gardama a ranar Lahadin da ta gabata.

A wani jawabi da yi a jiya Talata,wanda aka watsa a kafafen talbijin, basaraken, ya yi kiran hadin kai, yayin da dubban ‘yan kasar suka bazama akan tituna a arewa maso gabashin Lardin kasar, suna zanga zangar nuna adawa kan matakan da ‘yan sanda suka dauka na far ma wadanda suka fita yin zaben.

Shugabannin ‘yan aware a yankin na Catalonia, sun sha alwashin za su ayyana yankinsu a matsayi mai cin gashin kansa, duk da cewa hukumomin Madrid sun bayyana zaben a matsayin haramtacce.

Shugaban Catalan, Carles Puigdemont (kales pujdimond) ya fadawa BBC cewa ayyana ballewar yankin daga kasar ta Spain zai zo nan da wasu kwanaki masu zuwa.

Kungiyoyin kwadago a bangaren Catalonia, sun yi kiran da a gudanar da yajin aikin gama gari, domin nuna fushi kan yadda ‘yan sanda suka wulakanta mutanen da suka fita yin zaben

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG