A ranar 25, ga watan agusta da ya gabata ne aka kai hari akan ofisoshin ‘yan sanda da sansanonin sojoji a jihar Rakhine dake arewacin kasar, amma ba a bayyanawa ‘yan jarida da ‘yan rajin kare hakkokin bil’adama irin wadannan munanan abubuwan ba. Yara ne suka zana su.
Anthony Lake, shugaban hukumar tallafawa yara kanana ta majalisar dinkin duniya da ake kira UNICEF, ya fadawa manema labarai a Cox jiya Talata cewa, “a lokacin da suke aiki da yaran da suke kokarin taimakawa don su warware daga dimuwar da suka sami kansu ciki, daya daga cikin abin da suke yi shine sa yaran su zana hotuna.
Mr. Lake yace ya gani a wurare da yawa hotunan zanen dake nuna farin ciki daga yara, a wasu wuraren kuma, hotunan da muke gani sun sha bambam.
Hotunan da muke gani a nan munana ne. suna nuna irin abubuwan da bai kamata yaro ya gani ba, balle ma ya fuskancesu, a cewar Lake.
A wani hoton, wasu mutane da yaran suka zana a matsayin sojoji sun harbe fararen hula yayinda wasu kuma da tayiwu bata gari ne, suka yi amfani da takkubba suka caccaki wasu mutane da basa dauke da wani makami.
Facebook Forum