Kasa da mako daya da 'yanbindiga suka farma kauyen Izhige inda suka halla mutane fiye da dari sai gashi jiya sun sake farma kauyen.
WASHINGTON, DC —
'Yanbindiga sun sake kai hari a kauyen Izhige dake jihar Borno inda suka kara hallaka mutane kana suka kone abun da ya rage a kauyen.
Wayewar gari jiya Lahadi wasu 'yanbindiga suka sake farma Izhige. A wannan sabon harin 'yanbindigan sun kone wurin da mutanen garin ke samun ruwan sha da wasu wurare. Sun farma dattawan da suka samu. Sun kashe wasu kana suka yi gaba da wasu. Tun lokacin da aka kai harin farko kawo yanzu ba'a kai jami'an tsaro kauyen ba.
Mutanen da 'yanbindigan suka samu wannan karon wadanda suka koma ne su kwashe 'yan kayan da zasu iya samu daga gidajensu da aka rugurguza. Mutane sun gudu daga kauyen zuwa Gulak cikin jihar Adamawa dake makwaftaka da su. Wasu ma sun kaura zuwa Maiduguri ko Gwozah. Masu hali na zuwa su kwashe kayansu su yi gaba. Wadanda basu da hali kuma shi ke nan.
Yanzu dai garin ya zama fanko domin komi an kone har da abinci.

Your browser doesn’t support HTML5