WASHINGTON, DC —
Hukumar kwastam ta Najeriya, ta yi ma 'ya'yanta su fiye da dubu 45 karin girma a cikin shekarar da ta shige ta 2013, yayin da take kokarin daukar matakan dakile ayyukan masu fasa kwabri.
Kwanturola na hukumar Kwastam mai kula da jihohin Kwara, Kogi da Neja, Maitama Isiyaku Kura, yace a kullum masu aikin fasa kwabri sai sauya dabaru suke yi na satar shiga kasar da kayayyakin da aka haramta shiga da su, ko kuma wadanda ake kokarin shiga da su ba tare da an biya kudin fito ba.
Yace sau da dama, sun sha ganin motocin tanka na mai wadanda ba mai ne a ciki ba, kayan fasa kwabri ne.
A bara hukumar ta samarwa da gwamnatin Najeriya kudin shigar da ya kai Naira Tiriliyan Daya da miliyan dubu 2, kudin da bangaren man fetur ne kawai ya samar da wanda ya fi wannan a kasar.