Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Rufe Bakin Iyakar Jihar Adamawa Da Kasar Kamaru


An dauki wannan matakin a wani bangaren yunkurin farauto 'yan Boko Haram da suke kisan ta'addanci ma jama'a a garuruwan dake dab da bakin iyakar.

Hukumomin soja a Najeriya sun rufe dukkan iyakokin Najeriya da Kamaru a jihar Adamawa, a wani bangaren sabon yunkurin farauto 'yan bindigar kungiyar Boko Haram dake gudanar da kashe-kashen ta'addanci kan al'umma fararen hula a jihohin na Adamawa da Borno.

Haka kuma, an kara yawan sojoji a bakin iyakar jihohin Borno da Adamawa, domin kai farmaki a cikin dazuzzukan da aka yi imanin cewa 'yan bindigar na Boko Haram sun kafa sansanoni.

Kwamandan birged ta 23 ta askarawan Najeriya dake Yola, Birgediya-janar Rogers Nicolas, yace an dauki wannan matakin ne domin kawo karshen wadannan munanan hare-haren ta'addancin da 'yan Boko Haram ke kaiwa, ya kuma roki jama'a da su gaggauta sanar da sojoji da zarar sun gani ko sun ji motsin wadannan 'yan bindigar ta yadda sojojin zasu iya kai musu taimako cikin gaggawa.

Mutane da dama sun yi imani da cewa 'yan Boko Haram sun yi sansanoni cikin dazuzzukan dake iyaka da garuruwan Maiduguri, Konduga, Bama, Gwoza, Damboa da wasunsu, daga inda suke kai farmaki kan wadannan garuruwan.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG