Zaratan ‘yan matan dake wakiltar Najeriya a wassanin Olympics da ake a Koriya ta Kudu na dada samun farin jini a idon duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria yace ko sun sami nasara ko basu samu ba, ya shirya tsaf don karbar tawaggar ‘yanmatan nan hudu dake wakiltar Nigeria a wajen wassanin motsa jiki na Olympics wannan shekara da ake a birnin PyeongChang na Koriya ta Kudu. ‘Yan matan, wadanda suka hada da Seun Adigun, Ngozi Onwumere, Akuoma Omeoga da Simidele Adeagbo, wadanda dukkansu a Amurka aka haife su, suna kara samun kulawa ne ganin cewa, a sanadinsu, wannan ne karo na farko da Nigeria ta samu wakilci a wadanan wassanin da ake a cikin matsanancin sanyi.
Shrinmu na LABARAN WASSANI na wannan makon ya bada karin haske kan wadanan jaruman ‘yanmatan:
Your browser doesn’t support HTML5