Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Ta Bar Kofar Tattaunawa da Koriya ta Arewa A Bude


Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence (L) da Firayim Ministan Japan Shinzo Abe (R). Dukansu zasu kasance a wasannin a Koriya ta Kudu
Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence (L) da Firayim Ministan Japan Shinzo Abe (R). Dukansu zasu kasance a wasannin a Koriya ta Kudu

Wasan Olympics na hunturu da za'a fara a Koriya ta Kudu wannan makon na iya zama hanyar bada damar tattaunawa tsakanin jami'an gwamnatocin Amurka da Koriya ta Arewa saboda dukansu zasu kasance a wurin a wurin wasannin.

A halin yanzu kuma Gwamnatin shugaba Donald Trump na Amurka tace zata “bar kofa a bude” don yiyuwar ko za’a gana a tsakanin mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da jami’an gwamnatin Koriya ta Arewa, idan sun hadu a wajen wassanin motsa jiki na Olympics da za’a fara a wannan makon a Koriya ta Kudu.

Koda yake Pence yace bai nemi zama da jami’an na Koriya ta Arewa ba, yace zai je da shirinsa koda zaman ya kama ma yi shi.

Shima Sakataren harakokin Wajen Amurka Rex Tillerson irin kalamin da ya fada ke nan lokacinda aka yi mishi tambaya gameda ko za’ayi irin wannan ganawwar tsakanin jam’ian kasashen biyu.

Shugaban “je-ka-nayi-ka” na Koriya ta Arewa Kim Yong Nam ne zai yi jagoranci ga tawaggar ‘yan wasan Koriya ta Arewa da zasu halarci wadannan wassanin na Olympics a Koriya ta Kudu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG