Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Gasar Wasannin Olympics a Pyeonchang


Bikin bude gasar wasannin Olympics a Pyeongchang, Korea ta Kudu
Bikin bude gasar wasannin Olympics a Pyeongchang, Korea ta Kudu

A yau Juma'a aka bude gasar wasannin Olympics a birnin Pyeonchang na kasar Korea ta Kudu, wacce take takara a gasar a karkashin tuta daya da makwabciyarta Korea ta Arewa da ba sa ga maciji.

A Hukumance, an bude gasar wasannin Olympics a yau a Birnin Pyeonchang da ke Korea ta Kudu.

Masu sha’awar wasannin, sun nuna dauriya, inda suka fita duk da sanyin da ake fama da shi, domin su kalli wasannin wuta da aka yi.

Tawagogin 'yan wasa sun guadanar da fareti yayin da suke shiga filin wasan.

Babu tantama, masu lura da al’amura sun ce wasannin na Olympics, zai zo da abubuwan ja hankali, inda ake ganin hadin kan da Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, zai kasance babban lamari.

A daya bangaren kuma, da safiyar yau Juma’a mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya isa Birnin na Pyeonchang domin halartar wasannin bude gasar, inda ya gana da ‘yan Korea ta Arewa da suka bijirewa gwamnati suka sauya sheka.

Jami’an Amurka, sun ce babu yiwuwar Mataikamin shugaban kasar na Amurka zai gana da jami’an Korea ta Arewa a wajen wasannin na Olympics.

Ita ma kafar yada labaran Korea ta Arewa a ranar Alhamis, ta ruwaito cewa, babu wata alama da ke nuna cewa jami’an Korea ta Arewan za su nemi a gana.

Hakan na faruwa ne yayin da ‘yar uwar shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ta isa Korea ta Kudu domin halartar gasar.

Ita ce ta farko daga ciki iyalan da suka dade suna mulkin kasar ta Korea ta Arewa, da ta ziyarci Korea ta Kudu, tun bayan karshen yakin Korea da aka yi daga shekarar 1950 zuwa da 1953.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG