Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea ta Arewa Ta Gudanar Da Gagarumin Faretin Soji


Sojojin Korea Ta Arewa yayin a suke gudanar da gagarumin fareti.
Sojojin Korea Ta Arewa yayin a suke gudanar da gagarumin fareti.

Korea ta Arewa ta gudanar da wani gagarumin faretin soji da tankunanta na yaki, kwana daya kafin a soma wasannin motsa jiki na Olympics a makwabciyarta ta Kudu.

Kafofin yada labarai na gwamnati a Seoul sun ce dubban mutane ne suka halarci shagalin kallon wucewar mayakan da kayan yakin da aka gudanar a Dandalin Kim Il Sung da ke can Korea ta Arewan.

A halin yanzu kuma, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya tabattarwa al’ummar kasar Korea ta Kudu cewa Amurka za ta yi aiki da su wajen ci gaba da matsawa Korea ta Arewa lambar ta watsar da shirinta na neman kera makaman kare dangi na nukiliya da masu linzamai.

Pence ya yi wadannan kalaman ne yayin da yake isa Korea ta Kudu don halartar wasannin na Olympics da za’a soma gobe.

Rahotanni sun yi nuni da cewa Pence ya halarci wasannin ne don tabattar da ganin Korea ta Arewa ba ta janye hankalin duniya da maganar makamanta na nukiliya ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG