‘Yan uwan fasinjojin da aka yi garkuwa da su bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, sun nemi gwamnati da ta agaza musu wajen kubutar da ‘yan uwansu.
A farkon makon nan ne, ‘yan bindigar suka saki yi wasu sabbin hotunan mutum sama da 60, wadanda suka karade kafafen sada zumunta.
Sun saki hutunan ne cikin rukunna hudu wadanda suka hada da maza, mata da kuma yara kanana.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito shugaban kungiyar ‘yan uwan wadadan aka sace, AbdulFatai Jimoh yana cewa lallai mutanen da ke cikin hotunan fasinjojin da aka sace ne.
A ranar 28 ga watan Maris ‘yan ta’addan suka far wa jirgin cikin dare inda suka dasa masa bam akan turakunsa, suka kuma bude masa wuta.
Akalla fasinja 8 ne suka mutu a lokacin harin, wasu kuma da dama suka jikkata baya ga gomman mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ku Duba Wannan Ma Garkuwa Da Mutane Na Shafar Lafiyar Kwakwalwarsu - MasanaLamarin ya faru ne a daidai Katari da ke jihar Kaduna, kilomita 90 daga Abuja, babban Birnin kasar.
Shugaba Muhammad Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kubutar da mutanen, kamar yadda kakakinsa Malam Garba Shehu ya fadawa Muryar Amurka.
“Ceto ake so a yi, ba wai a hallaka wadanda ake rike da su ba da su kansu ‘yan ta’adda, idan munafar ita ce, a je a kai hari a hallaka kowa da kowa, su jami’an tsaro sun ce da tuni an yi wannan.” In ji Shehu.
Ya kara da cewa, “su kansu iyalai da dangi za su fi jin dadi yayin da aka dawo musu da ‘yan uwansu da ransu ba a kawo musu gawarwaki ba.”
Sai dai masana a fannin tsaro, sun soki irin wannan umarni da shugaban yake yawan bayarwa, suna masu cewa ba kasafai yake tasiri ba.
A kwanakin baya, ‘yan ta’addan sun saki wani bidiyo dauke da wasu daga cikin fasinjojin inda suke ikirarin gwamnati ta san damuwarsu kuma ta biya musu ba tare da bata lokaci ba.