Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Iyayen Da Su Ka Rasu Cikin Shekaru 8 Da Garkuwa da 'Yan Matan Chibok


iyayen 'yan matan Chibok a wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a villa, Abuja, Nigeria, January 14, 2016 REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX22DYM
iyayen 'yan matan Chibok a wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a villa, Abuja, Nigeria, January 14, 2016 REUTERS/Afolabi Sotunde - RTX22DYM

Yau aka cika shekaru takwas da kungiyar Boko Haram ta sace dalibai mata 276 a wata makarantar kwana da ke garin Chibok, jihar Borno.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar ‘al’ummar Chibok mazauna birnin tarayya Abuja, daya daga cikin wadanda suke kai ruwa suna kai mari domin matsawa gwamnati lamba ta ceto ‘yan matan, ya bayyana cewa, I zuwa yanzu, iyaye talatin da takwas sun mutu sakamakon bakin ciki da damuwar rashin ceto ‘ya’yansu. Ya kuma ce akwai biyu daga cikin iyayen da ko bayanda kungiyar ta sace ‘ya’yansu, ta kuma ta kashe su a wani hari dabam.

Bisa ga cewar shi, muhimman abubuwa biyu da suka dami iyayen shi ne rashin dawowar ‘ya’yansu da kuma rashin tsaro da al’ummar yankin ke fama da shi tun kafin sace ‘yan matan.

Mallam Nkeki Mutur ya bayyana cewa, I zuwa yanzu ‘yan matan dari da tara ne har yanzu su ke hannun kungiyar Boko Haram, kasancewa kimanin makonni biyu da su ka shige, sun sami labarin cewa, an gano daya daga cikin daliban wadda ta sami tserewa, yanzu haka kuma tana hannun gwamnati duk da yake gwamnati ba ta tuntubi iyayen ko shugabannin al’ummar ba domin sanar da su. Ya ce dalili ke nan da ya sa su ke ci gaba da kirga sauran daliban da ba su yi ido hudu da su ba a matsayin wandada ake ci gaba da garkuwa da su.

Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja
Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja

Shugaban kungiyar al’ummar Chibok din ya bayyana cewa, gwamnati ba ta tuntubar iyaye ko yin wani bayani dangane da bacewar ‘yan matan sai bayan kungiyar ta tada batun ko kuma ta kira taron manema labarai kafin gwamnati ta yi wata magana a kai domin dauke hankalin jama’a da kokarin nuna cewa tana wani abu a kai duk da yake a zahiri ba bu abinda ta ke yi.

A nata bayanin, Madam Martha Bitrus Dalu wata ‘yar asalin garin Chibok da ta gudanar da cikakken bincike ta kuma rubuta littafi kan sace ‘yan matan, ta ce duk da yake suna kyautata zaton kungiyar ta ci zarafin dukan daliban, kuma yana yiwuwa dukan su sun haihu a tsawon shekarun nan takwas, sai dai suna daukar su a matsayin ‘yan mata da ke da guri a rayuwa da kuma za a iya taimako su cimma gurin su. Ta ce a shirye su ke su rungume su da ‘ya’yan da su ka haifa idan aka sami ceto su.

Sun kuma bayyana niyar ci gaba da fafatuka da jan hankalin duniya, da kuma matsawa gwamnati lamba sai an dawo da sauran ‘yan matan da ke da rai.

Daliban makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su
Daliban makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su

Daga cikin ‘yan mata 276 da kungiyar ta sace da asubahin 14 ga Afrilu, 57 sun kubuta ba da dadewa ba bayan garkuwa da su, yayinda kungiyar da saki dalibai 107 bayan tattaunawa da gwamnati da kungiyar ta nemi yin musayar fursunoni da ‘yan matan. Daga baya kuma wadansu dalibai uku suka tsere daga sansanin kungiyar suka kubuta da goyo.

A hirar ta da Muryar Amurka, daya daga cikin daliban ta bayyana yadda ta gudu da ciki ta shiga nakuda a jeji ta kuma haihu jaririn ya mutu a kan hanya sabili da tsananin wahala. Bisa ga cewar ta bayan rasuwar jinjirin, sai ta rufe shi da ganye ta ci gaba da gudu da danyen jego domin ceton ranta, ta bar gawar a gindin itace.

‘Yar Majalisar Wakilan Amurka Frederica Wilson ta jagoranci gangamin tada tsimin al’umma da kuma matsawa gwamnatin Nageria lamba ta ceto sauran daliban, da ya hada da jagorantar tawagar ‘yan majalisa zuwa Najeriya, da kuma tsokaci a hanyar sadarwar internet kowacce ranar Laraba da nufin jan hankalin al’umma kan bukatar ceto sauran ‘yan matan.

Wadansu 'yan matan Chibok tare da Frederica Wilson da wadansu 'yan majalisar dokokin Amurka
Wadansu 'yan matan Chibok tare da Frederica Wilson da wadansu 'yan majalisar dokokin Amurka

Wasu kungiyoyin jinkai sun dauki nauyin ilimantar da wadansu daga cikin daliban da su ka kubuta, da su ka hada da Joy Bishara da Lydia Pogu, biyu daga cikin kimanin dalibai 10 da wata kungiya ta kawo Amurka, wadanda tuni su ka kammala jami’a.

Watanni bayan ceto ‘yan matan na Chibok 107, gwamnati ta tura su ci gaba da karatu a jami’ar American mai zaman kanta da ke Yola, jihar Adamawa.

Ganawar Shugaba Trump da 'yammatan Chibok
Ganawar Shugaba Trump da 'yammatan Chibok

Tun lokacin da aka sace ‘yan matan aka kafa kungiyoyi da dama a ciki da wajen Najeriya da nufin jawo hankalin gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta tashi tsaye a yunkurin ceton ‘yan matan.

Mawakiya, Alicia Key, da masu zanga-zangar neman kubuto da 'yan kubuto da 'yan mata fiye da 200, da 'yan Boko Haram suka sace watani 6, da suka wuce, 14 ga Oktoba 2014.
Mawakiya, Alicia Key, da masu zanga-zangar neman kubuto da 'yan kubuto da 'yan mata fiye da 200, da 'yan Boko Haram suka sace watani 6, da suka wuce, 14 ga Oktoba 2014.

Daya daga cikin kungiyoyin ta yi fafatukar neman ceto ‘yan matan tun da aka sace su da taken #BringBackOurGirls, da ya dauki hankalin kasashen duniya, da suka hada da mai dakin shugaban Amurka na lokacin Michelle Obama.

An sace ‘yammatan ne ranar 14 ga watan Afrilu shekara ta dubu biyu da goma sha hudu a wata makarantar sakandare ta kwana da ke garin Chibok, inda aka tara su domin daukar jarabawa, bayan rufe makarantu a jihar sakamakon rashin tsaro.

Tun kafin sace ‘yan matan, al’ummar Chibok da wadansu kauyuka a jihar Borno sun yi ta korafin cewa, kungiyar na daukar ‘ya’yan su mata dai-dai sai dai ba su sami jan hankalin hukumomi ba.

Tun bayan sace ‘yan matan Chibok, kungiyar Boko Haram da wadansu kungiyoyin ‘yan bindiga da ake fama da su a Najeriya su ke ci gaba da sace jama’a da neman kudin fansa, da su ka hada da daruruwan dalibai da aka sace daga makarantun kwanan su.

Masu gangamin ceto 'yan matan Chibok da taken #BringBackOurGirls
Masu gangamin ceto 'yan matan Chibok da taken #BringBackOurGirls

Jerin kai hare hare a makarantu da garkuwa da dalibai da kungiyoyin ta’addanci a Najeriya su ka yi, sun hada da sace ‘yan matan sakandare ta Dapchi 110 da kungiyar Boko Haram ta yi ranar 19 ga watan Fabrairu shekara ta 2018, shekaru hudu bayan garkuwa da daliban Chibok, kafin a watan Maris, ta sako dukan dabilan banda biyar da suka mutu a kan hanya lokacin da aka sace su, su ka rike daliba daya Leah Sharibu sabili da ta ki Musulunta kamar yadda su ka bukata ta yi, wadda har yanzu ta ke hannun kungiyar.

Kungiyar ta ci gaba da garkuwa da dalibai da neman kudin fansa a jihohi dabam dabam na arewacin Najeriya da su ka hada da jihohin Yobe, Kaduna, Zamfara, Katsina, Niger, da Kebbi.

Ko banda kai hari da garkuwa da dalibai a makarantu, kungiyoyin ‘yan bindiga suna kai hare hare da garkuwa da mutane a kauyuka da kuma kan hanyoyin arewacin kasar, da ya hada da hari na baya bayan nan kan jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, da ya yi sanadin mutuwar fasinjoji takwas, da jikkata wadansu, yayinda kungiyar ta yi garkuwa da fasinjoji da dama, wadanda har yanzu su ke hannun maharan da aka bayyana cewa, galibi matasa ne.

Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.
Mutanen da yan sandan jihar Zamfara ta kubutar daga hannun yan bindiga.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ceto ‘yan matan Chibok, da kuma shawo kan matsalar tsaro a lokacin da ya ke yakin neman zabe a shekara ta 2015, alkawarin da bai cika ba, a maimakon haka, matsalar tsaro ta kara ta’azzara a duk fadin kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG