'Yan Tawayen Libiya Sun Ce Su Ke Iko Da Zlitan

  • Ibrahim Garba

Shugaban Majalisar Wuccin Gadin Shugabanncin Libiya, Mustafa Abdel Jalil.

‘Yan tawayen Libya sun ce sun kwace garin Zlitan dake bangaren yammacin kasar,

‘Yan tawayen Libya sun ce sun kwace garin Zlitan dake bangaren yammacin kasar, a bayan mummunan fadan da suka gwabza da sojoji masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi.

‘Yan tawaye sun fada yau jumma’a cewa sun kutsa har tsakiyar garin mai tazarar kilomita 150 daga Tripoli. Ba a samu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskata wannan ikirarin ba. Suka ce an kashe mayaka akalla 30 a gwabzawar da sassan biyu suka yi.

‘Yan tawayen dake samun tallafin NATO, su na kara nausawa, sannan a hankali, zuwa Tripoli, babban birnin kasar. A halin da ake ciki, karar fashe-fashe ta jijjiga Tripoli, babban birnin Libya yau jumma’a, a lokacin da aka yi ruwan bama-bamai a kusa da gidan shugaba Muammar Gaddafi da wasu unguwanni da dama na birnin.

Kakakin gwamnatin Libya, Mousa Ibrahim, yayi Allah wadarai da kungiyar NATO wadda ta ke taimakawa ‘yan tawayen ta hanyar kai harin bama-bamai kan sojojin Gaddafi. Wannan Allah wadarai da Ibrahim yayi a yau jumma’a, ta zo ne a bayan da aka samu rahotannin cewa an kashe wani dan’uwansa a harin da jiragen saman NATO suka kai jiya alhamis a garin Zawiya.

A can garin na Zawiya kanta, sabon fada ya barke a tsakanin sojojin ‘yan tawaye da na Gaddafi. Jiya alhamis, ‘yan tawaye sun ce sun kwace wata matatar mai a Zawiya, sun kuma kama garin Sabratha dake yamma da