Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Na Bayyana Raayoyin Su Akan Shigar Yan Tawaye Birnin Tripoli


'Yan tawayen kasar Libiya sun isa birnin Tarabulus.
'Yan tawayen kasar Libiya sun isa birnin Tarabulus.

Birtaniya da Faransa da Amurka na ci gaba da furta raayoyin su akan juyin al'amura a kasar Libiya

Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron ya ce nasarar da ‘yan tawaye su ka yi, su ka shiga Tripoli babban birnin kasar Libiya ta taimakawa juyin juya halin yankin Gabas ta Tsakiya wajen fara kafa demokradiya a yankin.

Mr.Cameron ya fada a yau litinin cewa Birtaniya ta yi amanna, ta taimaka wajen hana yiwa bayin Allah kisan gilla a yankin, kuma ya ce Birtaniya ta na alfahari da rawar da ta taka a cikin juyin juya halin kasar Libiya. Ya ce nan kusa gwamnatin kasar Birtaniya za ta iya fara sakin kadarorin kasar Libiya da ke kasashen waje domin al’ummar kasar ta amfana.

Faransa tace nan gaba kadan shugaban ‘yan tawayen kasar Libiya zai je Paris. Faransa ce kasar da ta fara amincewa da Majalisar mulkin wucin gadin kasar Libiya a matsayin halastacciyar wakiliyar al’ummar kasar ta Libiya.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya yi kira ga shugaban kasar Libiya Moammar Ghadafi da ya yar da kwallon mangwaro ya huta da kuda.

A cikin wata sanarwar da ya gabatar da yammacin jiya lahadi bayan da ‘yan tawayen Libiya su ka isa Tripoli, Mr.Obama ya ce Mr.Ghadafi na bukatar sanin cewa ikon kasar ya kubuce ma sa.

Haka kuma Mr. Obama ya ce Amurka za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen duniya su tallafawa kasar Libiya ta girka tsarin demokradiya cikin lumana, sannan kuma ya yi kira ga Majalisar mulkin wucin gadin kasar da, ta yi la’akari da muradun illahirin al’ummar kasar Libiya.

Mustapha Abdel Jalil, Shugaban Majalisar mulkin wucin gadin kasar Libiya
Mustapha Abdel Jalil, Shugaban Majalisar mulkin wucin gadin kasar Libiya

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG