Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Libya Sun Ce Saura Kilomita 30 Su Isa Tungar Gaddafi


Mayakan 'yan tawayen Libya sun doshi Tripoli, babban birnin kasar, daga kauyen Mayah, mai tazarar kilomita 30 a yamma, lahadi 21 Agusta, 2011
Mayakan 'yan tawayen Libya sun doshi Tripoli, babban birnin kasar, daga kauyen Mayah, mai tazarar kilomita 30 a yamma, lahadi 21 Agusta, 2011

An yi ta jin fashe-fashe da harbe-harbe babu kaukautawa duk tsawon dare a Tripoli a yayin da ‘yan tawaye da kuma NATO suka yi ta kai hari kan birnin

‘Yan tawayen Libya, wadanda suka dirkaki Tripoli, babban birnin kasar, sun ce sun gwabza har zuwa kimanin kilomita 30 daga tungar shugaba Muammar Gaddafi, a bayan da aka shafe dare ana harbe-harbe da fashe-fashe.

‘Yan tawayen da suka doshi Tripoli tare da taimakon NATO daga garin Zawiya dake yamma da babban birnin, sun ce mayakan Gaddafi su na yi musu luguden wuta da rokoki da bindigogin kabo jiragen sama.

An yi ta jin fashe-fashe da harbe-harbe babu kaukautawa duk tsawon dare a Tripoli a yayin da ‘yan tawaye da kuma NATO suka yi ta kai hari kan birnin. Sa’o’i kafin nan, ‘yan tawayen sun ce sune ke iko da wasu muhimman garuruwa guda biyu, Zawiya a yamma da kuma Brega a gabashin Libya.

A cikin wani sako na sautin murya da aka watsa ta gidan telebijin na Libya, shugaba Muammar Gaddafi yayi kira ga magoya bayansa da su fito domin murkushe wannan tunzurin. Yayi watsi da wannan tawayen a zaman wani yunkurin da ba zai kai ko ina ba ga su ‘yan tawayen da ya bayyana a zaman "maciya amanar kasa, kuma beraye."

A wani jawabin dabam a yau lahadi, dan shugaban na Libya Seif al-Islam Gaddafi yace gwamnati ba zata watsar da yakin ba. Kakakin gwamnatin Libya, Mousa Ibrahim, ya musanta cewa gwamnatin Gaddafi tana dab da rushewa, ya kuma dora laifin wannan zub da jini na Libya a kan shugabannin kasashen yammaci. Yace gwamnatin Gaddafi tana da goyon baya sosai, kuma ya kamata dukkan bangarorin su fara yin aikin warware wannan batu ta hanyar lumana.

XS
SM
MD
LG