Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan tawaen Libya sun kutsa dandalin Green a birnin Tripoli


Wadannan mutane ne suka murna mamaye birnin Tripoli da yan tawaye suka yi.
Wadannan mutane ne suka murna mamaye birnin Tripoli da yan tawaye suka yi.

Mayakan yan tawayen Libya sun samu nasarar kutsawa zuwa dandalin green a tsakiyar birnin Tripoli, bayan da suka wuce kariyar da aka yiwa birnin. Sun kuma bada sanarwar cewa sun kama 'ya'yan shugaba Gaddafi guda biyu.

Mayakan yan tawayen Libya sun samu nasarar kutsawa dandalin green a tsakiyar birnin Tripoli. Sun kuma bada sanarwar cewa, sun kama 'ya'yan shugaba Moammar Gaddafi guda biyu, ciki wanda aka zaci zai gaje shi, Seif Al -Islam.

Turjewa kalilan sojojin yan tawaye da suka doshi birnin daga yammaci suka samu, a yayinda suka kutsa sansanonin gwamnati a wajen baban birnin kasar. Dubban mutane a birnin Tripoli ne suka yi ta murna a lokacinda mayakan masu hamaiya suka isa dandalin green, harma sun canjawa dandalin suna zuwa dandalin masu sadaukar da rai, inda yan Libya dake cike da murna suka yayyaga hotunan Gaddafi suka tattaka su. In baicin kwanan nan, gwamnatin kasar ta kan yi amfani da wannan yanki ko dandali wajen yin gangamin goyon bayan Gaddafi.

Da sanyin safiyar yau litinin, shugabanin 'yan tawaye suka tabbatar cewa har yanzu suna yin kicibis da turjewa kadaran kadahan a ciki da kewayen birnin Tripoli. Mai magana da yawun 'yan tawaye yace mayaka sun yiwa ginin Bab Al Aziziya inda suke kyautata zaton kila Mr Gaddafi yana ciki, kofar rago, to amma kuma suna dari darin kai sumame akan gidan gadan gadan.

Mai magana da yawun 'yan tawaye yace an tura wasu mayaka zuwa cikin birnin ta teku daga tashar jiragen ruwan Misrata. Haka kuma yace, zaratan sojojin da aka dorawa alhakin kare Gaddafi sunyi saranda, matakin daya baiwa masu hamaiya damar mamaye yawancin yankuna ko kuma unguwanin birnin.

Tunda farko kotun kasa da kasa dake shari'ar wadanda suka aikata laifuffukan yaki, ta tabbatar da cewa an kama Seif Al Islam. Za'a tuhume shi tare da mahaifinsa da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar akan zarge zargen aikatawa Bani adamu laifi da kuma zargin cewa sun bada umarni ba bisa ka'ida ba aka kaiwa farar hula hare hare a farko farkon ranakun murkushe masu zanga zangar kin jinin manufofin gwamnati da karfin tsiya.

Jiya lahadi lauyan kotun kasa da kasa ICC Luis Moreno Ocampo yace, ya kamata nan bada jimawa ba an danka Seif Al Islam hannun kotun kasa da kasa a Hague kasar Netherlands ko Holland. A halin da ake ciki kuma, shugabanin masu hamaiya sun fadawa manema labaru cewa baban dan Gaddafi mai suna Mohammed yayi saranda ga sojojin 'yan tawaye.

Jiya gidan talibjijn na Libya ya gabatar da sakonin vidiyo na bijirewa daga Gaddafi. A daya daga cikin irin wadannan sakoni, Gaddafi ya tabbatar cewa yan tawaye sun doshi birnin Tripoli kuma yayi kashedin cewa idan ba'a yi hankali ba, birnin zai zama kamar birnin Bagadaza na kasar Iraq.

XS
SM
MD
LG