'Yan Ta'adda Sun Farwa Sojoji

Abubakar Shekau, Mayu 5, 2014 (Bidiyo)

An ga 'yan ta'adda akan mashina fiye da arbain akan iyakan Najeriya Kamaru, inda suka kaiwa wani Ofishin Sojoji hari, har suka kwashi makamai masu yawa.
Dangane da yara daliban Cibok da ‘yan boko haram suka sace babu abinda kasar Kamaru dace.

Sai dai akwai rade-radin cewa ana ganin wasu wadanda ake tsammanin ko ‘yan boko haram ne inji wakilin Muryar Amurka dake kasar Kamaru Muhammadu Danda.

Yace akan mashin sama da guda arbain suka zo da misalin karfe biyu na dare, domin kaiwa wani ofishin sojoji a garin kusiri hari wanda ke da iyaka da Chadi da Kamaru, a arewacin Najeriya.

Inda suka yi harbe-harbe suka kuma kwashi makamai da albarusai masu yawa, kuma sun samu nasaran kubutar da wani nasu da ake tsare da shi a wurin.

Akan harin da aka kai Gamboru Ngala kuwa cewa yayi ”abunda ya shafi Najeriya ya shafi Kamaru saboda Gamboru baida nisa da kasr Kamaru ‘yan Kamaru sunanan saune a kasar Najeriya, hakan nan ma ta sashen Kamaru akwai 'yan Najeriya,irin wadannan abubuwan dake faruwa a gaskiya yana tada hankali domin kuwa duk wadanda suke kan iyaka abun ya tayar masu da hankali duk da matakan tsaro da gwamnati ke cewa tana yi,alhalin sojoji sun yi karanci a cikin kasar Kamaru.”

Ya kara da cewa sojoji akasarin su basu son aiki akan iyaka domin gudun far masu da ake yi masu akan iyaka na ba zata.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kaiwa Ofishin Sojoji Hari - 2'16"