Rundunar 'yan sandan jihar Yobe tace ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 19 da ya tuka mota cike da bamabamai da yayi niyar kutsawa cikin harabar 'yan sandan. Kwamishanan 'yan sandan jihar Sanusi Rufai shi ya shaidawa wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Muhammed Fawu yadda lamarin ya faru.
Jiya Lahadi da safe da misalin karfe takwas da wasu mintoci wani Abubakar Sadiq Umar dan shekara 19 da haihuwa ya tuko mota akori kura dauke da ciyawa ta dabbobi amma a karkashin ciyawar an shirya bamabamai. Ya yiwo kukan kura yana son ya shiga ofishin 'yan sandan. Da suka tsayar dashi sai ya ki tsayawa su kuma suka harba bindiga lamarin da ya bashi tsoro. Sai ya fita da gudu amma aka kamashi. Suna bincikar motar sai suka ga bamabamai da aka shirya.
A cikin firar da suka yi da yaron ya fadawa 'yan sanda cewa wajen wata uku ake nan da 'yan Boko Haram suka sameshi a Talala cikin jihar Borno suka horas da shi daga bisani kuma suka turoshi ya aiwatar da ta'adancin.
Bangaren 'yan sanda dake kula da bamabamai ya lalata bamabaman da yaron ya tuko cikin mota.
Mazauna garin Damaturu sun ce suna zaman lafiya, babu wata matsala. Kowa yana walwala kodayake an tsaurara matakan tsaro.
Ga rahoton Sa'adatu Muhammed Fawu.