'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojojin Nijar 29 A Kan Iyakar Nijar Da Mali

Sojojin Kasar Nijar

Akalla sojojin Nijar 29 ne 'yan ta'adda suka kashe a kusa da kan iyakar kasar da Mali, in ji rundunar sojan Nijar a yayin da suke kokarin kawo karshen hare-haren mayakan.

WASHINGTON, D. C. - Fiye da 'yan ta'adda 100 ne suka yi amfani da bama-baman da aka hada a gida wajen kai hari kan jami'an tsaron na Nijar da aka tura yankin iyakar kasar, don fatattakar mayakan, in ji Ministan Tsaron Nijar Laftanar Janar Salifou Mody a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin. Wannan shi ne hari na biyu da aka kai wa sojojin Nijar cikin mako guda.

Wata guda bayan da sojojin Nijar suka kwace mulki, tashin hankali mai alaka da masu tsattsauran ra'ayi ya karu fiye da kashi 40 cikin 100, a cewar shirin ACLED da ke sa ido kan tashe-tashen hankula da tarzoma. Hare-haren da mayakan ke kai wa kan farar hula ya linka har sau hudu a cikin watan Agusta idan aka kwatanta da watan Yuli, haka kuma hare-hare kan jami'an tsaro a yankin Tillaberi sun karu, inda aka kashe sojoji akalla 40, in ji shirin.

"Abin takaici wannan harin ya janyo mutuwar zaratan sojojinmu da yawa," in ji Mody a ranar Litinin.

Nigar

Ya sake maimaita ikirarin da aka yi a baya na cewa "kasashen ketare da hadin bakin wasu ‘yan Nijar masu cin amanar kasa ana kai hare-haren hana zaman lafiya," ba tare da yin karin bayani ko ba da hujja ba.

Saboda matsin lambar da ake ci gaba da yi tun bayan juyin mulkin da aka yi wa shugaban Nijar Mohamed Bazoum, wanda sojojin suka ce sun yi shi ne saboda kalubalen tsaro da Nijar ke fuskanta, gwamnatin mulkin sojan ta yi alkawarin cewa "za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron mutane da dukiyoyinsu a fadin kasar."

-AP