'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojoji A Kasar Mali Tare Da Jikata Wasu

Sojojin kasar Mali

Wasu tagwayen boma-bomai sun tashi da wasu sojoji a tsakiyar Mali, cikin dare da suka yi sanadin mutuwar sojojin 6, da wasu da ake zargin ‘yan ta’addan ne 30 a daren jiya Lahadi, a cewar sojojin.

Harin dai an kai shi ne a sansanin sojojin da ke bakin iyakar kasar da Burkina Faso, inda aka taba kai hari akan ‘yan ta’addan a arewacin Mali a 2012, kamun daga baya suka watsu zuwa sauran wurare.

An tabbatar da mutuwar sojoji 6 da wasu 18 da suka samu rauni, a wata sanarwa da sojojin suka fitar. Harin ya kai ga mutuwar suma ‘yan ta’addan kusan 30.

Hare-haren dai sun faru ne a Boulkessy da Mondoro da ke tsakiyar kasar.

Kana bama-baman sun tashi lokacin daya da misalin karfe 3:30 na tsakar dare, a cewar sojojin, an cigaba da gwabza fada har na tsawon sa’a daya bayan hare-haren.

An kwace babura 40 da wasu kayan sojoji masu tarin yawa a hannun maharani, a cewar rundunar sojin.

An Kwashe sojoji da dama da suka ji rauni da jirgi mai saukar ungulu, a cewar wata majiyar kiwon lafiya.

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ya yi zama a farkon wannan domin maida hankali a kan rikicin kasar Mali da yaki-ci-yaki-cinyewa.

Babban sakatern MDD Antonio Guterres ya bayyana damuwar sa a kan tabarbarewa sha’anin tsaro, yana mai nuni da halin damuwa da ake ciki a tsakiyar kasar Mali.