Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Kashe Madugun Kungiyar 'Yan Tawayen Mali


Sojojin Faransa
Sojojin Faransa

Sojojin kasa da jiragen sojoji mai saukar ungulu sun kashe wani kwamandan mayakan jihadi masu alaka da al-Qaida a Mali tare da wasu mutum hudu, a cewar ma’aikatar sojin Faransa a jiya Juma’a.

Aikin da aka gudanar a ranar Talata, ya auna Bah ag Moussa, shugaban sojojin kungiyar masu tsaurin ra’ayin Islama ta RVIM, wanda yake cikin jerin mutanen da Majalisar Dinkin Duniya ta aza musu takunkumi kana ana sa rana yana da hannu a hare hare da dama a kan sojojin Mali da na kasashen waje dake cikin kasar, a cewar mai Magana da yawun ma’aikatar sojin Faransa, Kanal Frederic Barbry yana fadawa manema labarai a jiya Juma’a.

Jirage marasa matuka dake shawagi sun taimakawa sojojin Faransa a Mali wurin gano babbar motar Moussa a yankin Menaka dake gabashin Mali, kana jirage masu saukar ungulu suka auna shi wanda zaratan sojojin Faransa 15 suka kai wurin inji Barby. Ya ce an kashe duk mutum biyar dake cikin babbar motar bayan da suka yi watsi da harbin gargadi kana suka bude wuta a kan sojojin Faransan.

Ya kwatanta abin da mayakan suka yi da “kare kai ta yadda bai kamata” kana an bada gawarwakin su karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa. Sai dai bai yi wani karin bayani a kan ko sojojin kawance kamar na Amurka sun taimaka wurin wannan aiki.

Wata sanarwar daga ministan tsaron Faransa na cewa Moussa shine ke horar da sababbin mayakan jihadin. Wannan shine na baya a cikin jerin ayyukan da Faransa ke kaddamarwa a Mali a cikin ‘yan makwannin nan dake kashe mutanen da ake zaton masu tsaurin ra’ayi ne.

Moussa mayaki kungiyar ‘yan tawayen Tuareg ne mai kusanci da kwamandan mayakan jihadi Ag Ghaly, a lokacin da ‘yan ta’addan da sojojin ‘yan tawayen suka kwace ikon arewacin Mali a shekarar 2012. Hakan ne kuma yasa rundunar hakada karkashin jagorancin Faransa a shekarar 2013 ta ceto Mali daga rikici.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG