'Yan Ta'adda Sun Kashe Gomman Mutane A Mali, In ji Hukumomin Kasar

Kanar Assimi na kasar Mali

Gwamnatin rikon kwaryar Mali ta tabbatar da rasuwar fararen hula sama da 100 sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai a wasu kauyukan tsakiyar kasar a karshen mako sai dai wani dan siyasar yankin da abin ya faru na cewa yawan wadanda aka kashe ya haura 200.

Sai dai ana kallonsa lamarin a matsayin wani yunkurin hana manoma gudanar da aiki a daidai lokacin da aka fara samun saukar ruwan damana.

A sanarwar da suka bayar a jiya, hukumomin kasar ta Mali sun ce ‘yan ta’adda sun kai hare hare a garuruwan Dialassagou da Dianweli da Dedguessagou na yankin Bankass a tsakiyar kasar inda suka kashe mutane a kalla 132. Hukumomin sun dora alhakin wadannan kashe kashe a wuyan kungiyar Katiba de la Macina ta Amadou Kounfa.

Sai dai wani dan siyasa dan asalin yankin na Bankass Nouhoum Togo ya bayyana wa sashen faransanci na muryar Amurka cewa yawan wadanda aka kashe a wadanan jerin hare hare ya fi haka…

Ya ce a ranar Juma’a a wajejen karfe 4 zuwa 5 na yamma aka sanar da ni cewa an kai hari a kauyenmu Dialassagou inda ‘yan ta’adda suka shiga kasuwa suka kwashi ganima kafin su cinna wuta sannan suka bi gida gida suka tattara matasa suka fice da su bayan gari inda suka bindige su.

A cewarsa a jiya Litinin an wuni ana kwashe gawawaki inda a wannan gari aka tattara gawa sama da 80 kuma akwai wadanda ake ci gaba da neman gawawakinsu .

A Dibali kilomita kadan da Dialassagou an tarar da gawawaki 52 sannan a wani kauyen dake kusa da nan an samu gawawaki 46 wato dai a jimilce a na iya cewa gawawaki 180 zuwa 190 ne aka gano kuma ana ci gaba da jana’iza ana ci gaba da neman gawawaki.

Ya kara da cewa wannan wata dabara ce da ‘yan ta’adda ke amfani da ita don tsoratar da jama’a su kauracewa gonaki domin kauyen Dialassagou ana daukansa a matsayin rumbun cimakar wannan yanki. Kashi 80 daga cikin 100 na ‘yan Mali mutane ne da suka dogara da noman damana saboda haka wadanan hare hare wani yunkuri ne na haddasa karancin abinci a kasar.

Kasar Mali wace ta bada sanarwar ficewa daga kungiyar G5 sahel a watan Afrilun da ya gabata a dai gefe ta raba gari da rundunar Barkhane saboda zargin sojojin na Faransa da gaza murkushe matsalolin ta’addancin da ake fama da su a yankin Sahel kafin ta juya harakokinta wajen kasar Russia da nufin neman mafita sai dai da alama har yanzu tsugune ba ta kare ba.

Ga rahoton Souley Moumouni Barma daga birnin Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Ta'adda Sun Kashe Sama Da Mutane 130 A Kasar Mali, Inji Hukumomin Kasar.MP3