Ana Ce-ce-ku-ce Kan Zargin Gwamnatin Bazoum Da Jefa Nijar Cikin Kangin Bashi

Firai Ministan Rikon Kwarya Na Nijar Ali Mahaman Zeine Ya Tarbi Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancon Janar Abdulsalam Abubabakar

‘Yan siyasa da jami’an fafutuka a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar kasar ya sanar cewa Gwamnatin da soja suka hambarar a watan Yulin da ya gabata ta ci dimbin bashi daga ciki da wajen kasar.

NIAMEY, NIGER - A yayin da wasu ke nuna rashin jin dadinsu akan wannan al’amari wasu kuwa na ganin Firai Ministan ya fadi son ransa ne watakila da nufin samun karbuwa a wajen ‘yan kasar.

Milliard ko billion 5200 na cfa ne Firai Minista mai mukamin Ministan kudi Lamine Zeine ya bayyana cewa Gwamnatin da aka hambarar ta ci a matsayin bashi galibi daga waje, abinda wani ‘dan rajin kare hakkin ‘dan adam Abdou Idi na kungiyar FSCN ya ce bai yi mamakin jin wannan labari ba.

Firai Ministan ya tunatar da cewa miliard 300 na cfa kacal ne ake bin Nijar a shekarar 2010 wato a washegarin juyin mulkin da soja suka yi wa Gwamnatin tazarce sai dai wani tsohon ‘dan Majalissar Dokokin kasa Abdoul Moumouni Ghousmane na danganta al’amarin da sauyin da aka samu a fannin tattalin arzikin Nijar daga wancan zamani kawo yanzu.

Da yake amsa tambaya kan batun shirin gurfanar da mutanen da ake zargi da tafka ta’asa, Lamine Zeine ya ce za su damka komai a hannun mashara’anta domin ta yi bincike, to amma wani matashi ‘dan siyasa Chaibou Mohamed na cewa ba su da fargaba akan wannan kudiri kuma watakila ma allura za ta tono garma inji shi.

A dangane dan makomar tsohon Shugaban Majalissar Dokokin kasa Hama Amadou wanda daga kurkukun da yake tsare ya tafi ketare a shekarar 2021 don neman magani, Firai Ministan gwamnatin rikon kwarya Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce suna marhabin da duk wani ‘dan Nijar da ke fatan bada gudunmowa a lamuran da suka shafi tafiyar kasa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ce-ce-ku-ce Kan Zargin Gwamnatin Bazoum Da Jefa Nijar Cikin Kangin Bashi.mp3