'Yan Shi'a sun janye zanga zangarsu a Bagdaza

Muqtada al-Sadar shugaban 'yan Shi'a na kasar Iraqi

A jiya Litinin kura ta lafa a birnin Bagdaza, biyo bayan tarin masu zanga-zangar da suka mamaye wata unguwar da ke da ofisoshin kasashen duniya tun ranar Asabar.

Daga baya masu zanga-zangar suka waste daga wajen. Sun bazama ne domin zuwa wani bikin addini da ‘yan Shi’a ke yi don girmama wani Shaihin Malamin karni na 15, Imam Moussa al-Khadim.

Shugaban masu zanga-zangar Muqtada al-Sadar ya sha alwashin zasu dawo wajen, wato unguwar da a nan Majalisar Dokokin kasar take, da ma mafi yawancin ofisoshin jakadancin kasashen duniya.

Wanda yace za su dawo domin matsa lamba ga ‘yan Majalisar kasar don su canza zaben da aka yi, ko kuma a sake shi. Mafi yawancin ‘yan majalisar sun bar wajen karshen makon da ya wuce.

Musamman lokacin da mabiya Muqtada din suka mamaye cikin majalisar, tare da bukatar sabuwar gwamnati. Ba dai tabbacin ranar da za su dawo da zanga-zangar ba.

Haka kuma wani Dan Majalisa Serwan Sereni ya fadawa Muryar Amurka cewa, taron gaggawar da Shugaban kasar Faud Masum da Firaminista Haider al-Abadi suka kira da shugabannin sojojin sa kan kasar ya kasa cimma matsaya.

Al-Sadr dai shine jagoran ‘yan Shi’ar kasar mai dawa’ar ‘yan kasanci, wanda ya shahara wajen yakar Sojin Amurka a Iraki.

Sannan ya fake da raunin mutanen kasar game da tabarbarewar siyasa da rashawar dake cikin siyasar kasar da masu mulki.