Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

IRAQ: Wasu 'Yanbindiga Sun Kama Mutane 18 a Bagadaza


Jami'an tsaro na gadi a wani kamfani kasar Turkiya a Iraqi inda 'yanbindiga suka sace mutane 18
Jami'an tsaro na gadi a wani kamfani kasar Turkiya a Iraqi inda 'yanbindiga suka sace mutane 18

A Iraqi wasu 'yan bindiga sanye da kayan soja sun kama wasu 'yan turkiyya su 18 yau a Bagadaza babban birnin kasar.

Wani kamfanin gine gine da ake kira Nurol Insaat, wanda yake gina dandalin wasanni a unguwar Habibiyya da galibin mazauna wurin 'yan shi'a ne dake arewa maso gabashin Bagadazan.

Da misalin karfe uku na asubahi ne 'yan binidgar suka kama ma'aikatan, bayan da suka fasa kofofi suka kwace makaman masu gadi.

Zuwa yanzu dai babu shaidar ko su wanene 'yan binidgar da kuma dalilin su.

PM Turkiyya Numan Kurtulmus yace hukumomin kasar suna tuntubar takwarorinsu dake Iraqi.

A bara mayakan sakai na ISIS sun kama 'yan kasar Turkiyya su 49 a ofishin jakadancin kasar dake birin Mosul suka yi garkuwa da su na tsawon wata uku, kamin daga bisanin su sake su, cikin wadada suka yi garkuwa da su har da jami'an difilomasiyya da sojoji da kuma yara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG