An kashe jami'an tsaron Iraq guda biyar a wani tagwayen harin bam a birnin Bagadaza. Jami'an soja sunce wani bam da aka boye a gefen hanya ya tashi a arewacin gundumar Adhamiya jiya lahadi, sa'anan kuma bam na biyu ya tashi a lokacinda jami'an tsaro suka kai dauki a wajen tashin bam na farko.
Jami'ai sun baiyana cewa tashin bama baman sun halaka jami'an soja biyu da sojoji uku, a yayinda kuma mutane goma suka ji rauni.
Wannan tarzoma ta faru ne a daidai lokacinda jami'an Amirka dana Iraq suke baiyana damuwa akan iyawar Iraq wajen tinkarar matakan tsaro bayan sojojin Amirka sun janye a karshen wannan shekara.
To amma kuma duk da haka, kamfanin dlancin labarun Faransa ya ambaci mataimakin shugaban Iraq, Tarq Al Hashemi yana fadin cewa janyewar sojoji Amirka zai sa a samu ingantuwar matakan tsaro a kasar. Jiya lahadin yace fadada wa'adin kasancewar sojojin Amirka a Iraq zai jawo matsala.
A ranar talata shugaban yan Shiya Moqtada Al Sadr yayi kashedin cewa idan Amirka ta kara lokacin kasancewar sojojinta a Iraq, zasu fuskanci bijirewa