Shedun gani da ido sun ce ‘Yan Sanda a Kasar Kamaru sun yi wa magoya bayan ‘yan adawa mutun 200 duka, wadanda da ke wajen gidan shugaban na ‘yan adawa Maurice Kamto inda yake tsare a gida na kusan wata guda. An tura ‘yan Sandar Kwamtar da tarzoma a wannan makon domin tarwatsa masu kira da a saki shugaban nasu. ‘Yan Sanda sun hana Kambo barin gidansa bayan ya shirya wata zanga zanga na kin jinin gwamnati a watan Satumba.
Wata mace da ba’a san ko wacece ba mai goyon bayan shugaban ‘yan adawa Maurice Kamto, ta kwabe tsirara a gaban gidan tana kuma kira a gaban tarin ‘yan sanda cewa daurin da akai masa na wata guda ba ya cikin ka’ida.
Matar, ‘yar shekaru kusan 50, tana ihu cewa ba zata tafi ba har sai ‘yan sanda sun saki Kamto yayi Magana da ita.
Tana daya daga cikin magaya bayan shugaban na ‘yan adawa 200 da suka taru a kofar gidan Kamto domin alhinin daurin talala na wata guda tun da ‘yan sanda suka mamaye gidan nasa suka jefa shi cikin kulle.
Wani daga cikin magoya bayan Kamto, Giselle Malongo tace ta zo ne daga yammacin birnin Bafoussam domin ta tambayi dalilin tsare shi a gida da akayi tun ranar 22 ga watan Satumba.
Tace ‘yan sanda suna raunata mutane sun kuma hana su ganin Kamto, mutumin da ta kira “Shugaban Kasarsu.” Malongo ta ce ‘yan Sanda dauke da makamai suna kwace wayoyin magoya baya wadanda ke kokarin daukar hotuna na karo da magoyan. Tace kuma sun hana mutane kai taimakon abinci wa Kamto da iyalanshi.
Wani dan Jarida ya sheda ‘yan sanda na duka da kare magoya bayan Kamto wadanda a cikin su masu kai tallafin abinci ne.
Kamto ya fusata sosai game da rashin barin mutane su kai mishi tallafin abinci bayan da suka tsare shi na kusan wata guda.
‘Yan Sandan Kamaru sun ki fitar da bayani akan wannan batu kuma sun ki amsa tambayoyin manema labaru.
Hukumomin basu ayyana Kamto a matsayin yana tsare ne a gida ba, amma ‘yan sanda sun ki barin shi ya fita daga gida tun bayan da ya shirya zanga zangar kin jinin gwamnati a duk fadin Kasar a watan satumba.