Jam’iyyun hamayya a Jamhuriyar Nijer sun kaddamar da wani littafi mai kunshe da bayanan da suka kira kura-kuren da suka gano a tsare-tsaren zaben gama garin da ake sa ran gudanarwa a kasar, daga karshen shekarar 2020 a yayin da shugabannin hukumar zabe ke kiran bangarorin siyasa su bata hadin kai don ganin komai ya gudana yadda ya dace.
Jan hankulan jama’ar cikin gida da na waje a game da yanayin da tsare-tsaren zaben Nijer ke gudana, shine makasudun rubuta wannan littafi da ake kira “Livre Blanc” wanda ta wani bangare ke matsayin wata hanyar wa yar da kan magoya bayan jam’iyun hamayya, kamar yadda kakakinsu Maman Sani Adamou ya yi wa wakilin Muryar Amurka Karin bayani jim kadan bayan kaddamar da littafin mai shafika 40.
Aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi hukumar zabe da kundin rajistar zabe na daga cikin bukatun da ‘yan adawa ke ci gaba da matsin lamba akansu, a cewar wani kusa a jam’iyar Moden Lumana, Lawali Salissou Leger, ya ce, mahimmancin wadanan bukatu ya kai matsayin da za a tsaya a gyara tafiya.
Da alama wannan yunkuri na ‘yan hamayya ya fara tasiri a akan magoya bayansu a cewar Ramatou Alele daya daga cikin mayakan jam’iyar MPN Kishin Kasa.
Yanzu haka ana iya cewa an shayo gangara a tsare-tsaren zaben gama garin da za a fara gudanarwa daga watan Disamba mai zuwa, yayin da bayanai ke nunin da cewa hukumomin Nijer sun fara yunkurin baiwa kungiyar OIF aikin tace kundin rajistar zaben kasar, a matsayin wani matakin share fagen soma buga katinan zabe.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum